‘Yan sanda sun fara binkice kan mutuwar wani yaro sakamakon yi masa allura

police 1 750x430 1
police 1 750x430 1

‘Yan sandan jihar Lagos zasu gudanar da binkice kan dalilin mutuwar wani yaro bayan ayi masa allura, wanda ake zargin cewa anyi allurar ne a wani asibiti dake unguwar Ogombo dake cikin jihar Lagos.

Maimagana da yawun yan sandan jihar Lagos, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Alhamis.

Hundeyin ya ce yan sandan sun sami labarin faruwar rasuwar yaron, amma har yanzu a hukumance ba’a sami kowa da hannu cikin mutuwar yaron ba.

“Ah tabbas mun sami labarin faruwar lamarin, baban yaron yazo offishin mu don kawo kara amma yake ya rubata rahoto.”

“Ma’aikatan asibitin suma sun zo ofishin mu basu rubuta komai ba, don mufutar duk ban garorin biyu haka yasa muka mika lamarin zuwa ga CID domin yin bikincen da ya dace.” Inji shi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaitu cewa a wani fefen video ya karade kafafen sada zumunta ya nuna wani mtum yana koka tare da korafe kan wata ma’aikaciayar lafiya ta kashe masa dan sa sakamakon yi masa allura, duk da cewa bai bayyana sunan ta ba a videon.

Ya ce ma’aikaciyar lafiyar tayiwa dansa allura guda hudu batare daya ci abinci ba, haka yasa dan sa ya mutu.

Haka kuma kamfanin dillancin labarai ya rawaitu yacce fefen video ya nuna gawar yaron da baban sa yana kuka a kusa da gawar.

(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here