Kotu Ta Dakatar Da Batun Tisa Keyar Shugaban Yan Sandan Nigeria Zuwa Gidan Yari 

IGP alkali
IGP alkali

Wata babban kotun tarayyar mai zamanta a Abuja, ta dakatar da hukunchin da aka yiwa shugaban yan sanda Nigeria na daurin wata uku a gidan ‘dan kande, Mai shari’a Bolaji Olajuwon, a cikin hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, ya ce akwai shaidu a gaban kotun ta da ke nuna cewa shugaban yan sandan ya bi umarnin kotun.

Umarnin kotun farkon dai shine a maido da Patrick Okoli, wanda aka yi wa ritayar dole daga aikin ‘yan sanda.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa alkalin kotun da ya yanke hukuncin yayi la’akari da yadda shugaban yan sanda ya bi umarnin kotu, yana mai cewa.

“Saboda cikakken bin umarnin kotu da kuma tabbacin tabbatar da cika umarnin, an ajiye umarnin, tare amsar rokon da shugaban yan sandan yayi ” injin kotun.

Mai shari’a Olajuwon, a hukuncin da ya yanke a ranar 29 ga watan Nuwamba, ya yanke wa IGP hukuncin daurin watanni uku a gidan yari, saboda ya ki bin hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a ranar 21 ga Oktoba, 2011, na mayar da wani dan sanda mai suna Okoli.”

Okoli ya yi ritayar dole ne a shekarar 1992 a lokacin da ya ke aiki a rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi a matsayin babban Sufeton ‘yan sanda (CSP) ta hukumar ‘yan sanda (PSC a yanzu).”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here