NBTE ta amince da sabbin kwasa-kwasan ND da HND a HAFEDPOLY Kazaure

Hussaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure

Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Tarayya, Hussaini Adamu da ke Kazaure a Jihar Jigawa (HAFEDPOLY), ta samu amincewar Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa (NBTE) domin fara koyar da ƙarin kwasa-kwasan Diploma ta Ƙasa (ND) da Babbar Diploma ta Ƙasa (HND).

Mukaddashin shugaban makarantar, Dakta Bashir Ahmad Danzomo ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a.Inda ya ce amincewar za ta ƙarfafa makarantar ta fuskar ilimi tare da bai wa ɗalibai ƙwarewar aiki da za ta taimaka musu wajen samun aikin yi da dogaro da kai.

Ya yaba wa hukumar NBTE da tawagar da ta gudanar da aikin tantancewa, tare da tabbatar da cewa makarantar za ta ci gaba da kiyaye ƙa’idojin ilimi.

SolaceBase ta ruwaito cewa shugabar majalisar gudanarwar makarantar, Dakta Jummai Kperoge, ta ce sabbin kwasa-kwasan za su ƙara wa makarantar daraja ta fuskar ilimi, tare da jawo ɗalibai daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Kwasa-kwasan ND da aka amince da su sun haɗa da Aikin Jarida, Injiniyan Gine-gine, Injiniyan Inji, Gudanar da Harkokin Gwamnati, Kasuwanci, fannonin lissafin kuɗi, Ɗinki, Fasahar Polymer, Laburare da Bayanai, Banki da Kuɗi da Gudanar da Otal-otal da Baƙi.

A matakin HND kuma, kwasa-kwasan sun haɗa da Aikin Jarida da Ilimin Kafofin Yaɗa Labarai, Laburare da Bayanai, Fasahar Polymer, Ɗinki, Ƙididdiga,Lissafin Kuɗi, Tsare-tsaren Birane da Yankuna, Injiniyan Gine-gine da Fasahar Zane-zanen Gine-gine.

Haka kuma, NBTE ta amince da fara koyar da kwasa-kwasan ND a fannonin Fasahar Kiwon Lafiyar Jama’a, Fasahar Kiwon Lafiyar Al’umma da Fasahar Lafiyar Muhalli a Shahen Kimiyar Lafiya.

A Shahen Noma kuwa, hukumar ta amince da kwasa-kwasan Fasahar Lafiyar Dabbobi da Fasahar Samar da Kayayyakin Noma.

Shugabannin makarantar sun bayyana amincewar a matsayin babban ci gaba wajen bunƙasa ƙwarewar sana’o’i da ƙoƙarin shirya ɗaliban da suka kammala karatu domin samun aikin yi da dogaro da kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here