Wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani mazaunin gari tare da yin garkuwa da mutane tara, ciki har da matarsa da ’ya’yansa biyu, a unguwar Babban Saura (PW), dake ƙaramar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, lokacin da maharan suka kai hari gidaje uku a garin.
Read also: Sojoji sun sha alwashin shafe tarihin Bello Turji
Wani daga cikin al’ummar garin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) cewa maharan sun fara kai hari gidan wani dattijo, inda suka yi garkuwa da ’ya’yansa biyu.
Ya ce daga nan ne kuma suka wuce gidan wani mutum mai suna Sikiru, inda suka fasa katangar gidan suka shiga harabar gidan.
A cewarsa, Sikiru ya yi ƙoƙarin kare kansa lokacin da maharan suka shiga falonsa, inda suka yi gumurzu da wasu daga cikinsu.
Majiyar ta ce daga bisani ’yan bindigar sun harbe Sikiru har lahira, kafin su yi garkuwa da matarsa da ’ya’yansa biyu.
Ya ƙara da cewa maharan sun kuma shiga wani gidan da ke maƙwabtaka, inda suka yi garkuwa da wata mata da ’ya’yanta huɗu.
Daga baya, sojoji da haɗin gwiwae ’yan sa-kai sun yi nasarar kuɓutar da matar, wadda aka bayyana sunanta da Maman Mubarak, yayin da ’ya’yanta huɗu suke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwar.
Kwamandan ’yan sa-kai na yankin, Usman Adamu, ya tabbatar wa NAN faruwar lamarin, inda ya ce an fara yin garkuwa da mutane tara.
Read also: ‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da jami’in Kwastam tare da iyalansa a Zariya
Adamu ya ce ’yan sa-kai sun samu kiran gaggawa game da harin, nan take suka sanar da sojoji, waɗanda suka haɗa kai da su wajen bin sawun maharan.
“Mun samu kiran gaggawa cewa ’yan bindiga sun shiga Babban Saura PW, nan da nan muka sanar da sojoji, waɗanda suka haɗa kai da mu.
“Mun bi sawunsu har zuwa yankin Eastern Bypass, inda muka yi nasarar kuɓutar da wata mata mai suna Maman Mubarak, wadda ’ya’yanta huɗu ke cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.”
Ya ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin kuɓutar da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su, amma maharan sun tsere da su.
Wani mazaunin yankin, wanda ya bayyana sunansa da Anas, ya ce Sikiru ya kira shi ta waya bayan maharan sun shiga cikin garin.
NAN ta ruwaito cewa lokacin da wakilinta ya ziyarci yankin, masu ta’aziyya sun taru a gidan marigayin, yayin da mazauna yankin suka bayyana damuwarsu kan tabarbarewar tsaro.
Harin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai hari a wani gari da ke kusa da yankin, mai suna Kadaure, inda aka ruwaito cewa sun kashe wani mutum tare da satar shanu.
Read also: Sojoji sun sha alwashin shafe tarihin Bello Turji
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntuɓar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Mansur Hassan, ta wayar tarho ba.
Haka kuma, Hassan bai mayar da martani ga saƙon karta kwana da aka aika masa ba. (NAN)













































