Shugaban karamar hukuma a Zamfara da aka yi garkuwa da shi da wasu mutum 4 sun shaki ‘yanci bayan kwana 61 a Hannun masu garkuwa

Untitled design

Shugaban Karamar Hukumar Bungudu da aka yi garkuwa da shi a Zamfara, Nura Abdullahi, ya shaki iskar ‘yanci bayan kwana 61 a hannun masu garkuwa.

Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Laftanar Kanal Aliyu Danja, Jami’in yada labaran rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma (Operation FANSAN YAMMA) ya fitar a Gusau Zamfara a ranar Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa ‘yan fashin daji ne suka sace Abdullahi a ranar 25 ga Yulin 2026, yayin wani hari da suka kai gidansa da ke garin Bungudu.

NAN ta ruwaito cewa an kashe jami’an tsaronsa hudu, ‘yan sanda biyu da ‘yan banga biyu a gida, yayin musayar wuta da suka yi kafin su yi awon gaba da shi.

Danja ya ce shugaban da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su sun tsere daga hannun ‘yan ta’adda a safiyar ranar Alhamis.

A cewarsa, dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, sun karbi Shugaban Karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara, Hon. Nura Umar Abdullahi, da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su wadanda suka tsere daga hannun ‘yan ta’adda a safiyar ranar Alhamis, 24 ga Satumban 2026, a yankin Karamar Hukumar Kaura Namoda.

“An sace Hon. Nura Umar Abdullahi ne daga gidansa da ke garin Bungudu a watan Yulin 2026, wani lamari da Rundunar tsaro ta fitar da sanarwa akai a baya.

“Wadanda abin ya shafa sun tsere ne a yayin wani samame da sojoji suka kai bisa bayanan sirri a wani wuri da ake zargin ‘yan ta’adda ne a yankin, kuma sojojin da aka tura yankin ne suka karbe su.

“An ba su kariya ta tsaro kuma an kai su cibiyar kiwon lafiya ta soja, inda suke karbar magani kuma suna ci gaba da dua lafiyarsu da kuma yi musu tambayoyi,” in ji shi.

Danja ya bayyana cewa daya daga cikin wadanda abin ya shafa tuni ya koma ga iyalinsa, kuma ana shirye-shiryen hada sauran da iyalansu da Gwamnatin Jihar Zamfara kowanne.

“Rundunar ta yaba da jarumta, juriya da azamar wadanda abin ya shafa wajen samun ‘yancinsu bayan dogon lokaci a hannun masu garkuwa.

“Haka kuma ta yaba wa dakarunta kan jajircewar da kwazon da suka nuna wajen karba da kula da su.”

Ya tabbatar da cewa sojojin za su ci gaba da fatattakar ‘yan ta’adda a fadin yankin don gurgunta ayyukansu da kare al’ummomi.

Ya ce dakarun suna ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da dawowar wasu mutanen da har yanzu ake tsare ko kuma suka bace.

“Rundunar ta bukaci jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai akan lokaci ga rundunar sojoji mafi kusa ko wasu hukumomin tsaro,” in ji Danja. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here