Gwamna Yusuf ya hori mashawarta na musamman 27 su nuna biyayya da jajircewa gabanin zaben 2027

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci sabbin mashawarta na musamman 27 da aka nada da su nuna biyayya, jajircewa da tsayawa tsayin daka wajen gudanar da ayyukan da aka dora musu.

Ya bukace su da su marawa gwamnatin baya wajen cimma muradun tsarin habaka Kano (Kano First Agenda) da kuma na sabunta fata (Renewed Hope Agenda) na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Yusuf ya ba da wannan umarni ne ranar Alhamis a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar yayin rantsar da wadanda aka nada a Taron Majalisar Zartarwa karo na 41 da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa mutane 21 daga cikin wadanda aka nada sabbi ne, yayin da guda shida aka sake nada su bayan da suka yi murabus daga mukamansu da farko domin neman takara.

Ya kara da cewa jami’an da aka sake nadawa sun koma ma’aikatunsu ne sakamakon kwazonsu da kuma gudunmawar da suka bayar ga gwamnatin.

Jami’an da aka sake nadawa sun hada da Hon. Gambo Sallau, Musa Ado Tsamiya, Dr Danyaro Yakasai, Usman Bala Muhammad, Danladi Karfi da Umar Musa Gama.

Gwamna Yusuf ya ce an zabi sabbin jami’ai 21 ne dangane da cancanta, kyakkyawan tarihi na gudanar da aiki da kuma sadaukarwa ga manufofin gwamnatinsa.

Sabbin wadanda aka nada sun hada da Bello Nuhu Bello, Yahuza Adamu Yankaba, Ahmad Muhammad Aruwa, Buhari Sule Kura, Mustapha Buhari Bakwana, Hajiya Aisha Tamburawa, Abdulkadir Auwalu, Alawiyya Farouk da Ibrahim Hamisu Rimi.

Sauran sun hada da Ahmad Tijani Musa, Nasir Abdullahi Karaye, Mustapha Abdullahi Rabiu, Engr. Abdullahi Kutama, Hon. Ado Rabiu, Barr. Munir Dahiru Rimin Gado, Engr. Magaji Lambu, Muhammad Bashir Baffa, Auwalu Ibrahim Danzabuwa, Bello Lawan Bello, Abdulsamiu Tiamiu da Arc. Hauwa Hassan.

Gwamna Yusuf ya taya wadanda aka nada murna, ya kuma bukace su da su bayar da iyakacin gudummawarsu wajen yi wa al’ummar Jihar Kano hidima.

Yayin da suke magana a madadin wadanda aka nada, Engr. Abdullahi Kutama da Arc. Hauwa Hassan sun tabbatar wa Gwamnan cewa za su jajirce wajen sauke nauyin da ke kansu.

Taron rantsarwar ya sami halartar tsohon Mataimakin Gwamna, Abdullahi Gwarzo, tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha kuma Manajan Darakta na Hukumar Habaka Kogunan Hadejia-Jama’are, Rabiu Sulaiman Bichi da sauran manyan baki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here