Gwamnonin Arewa shida ne kadai suka goyawa Tinubu baya a 2023 – Shettima

SHETTIMA

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya ce gwamnonin Arewa shida ne kacal daga cikin 19 suka goyi bayan takarar Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.

Shettima ya fadi hakan ne a ranar Laraba a fadar Ibrahim Sulu Gambari, Sarkin Ilorin, yayin nadin AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan Kwara, a matsayin Sardaunan Masarautar Ilorin.

Sai dai bai ambaci sunayen gwamnonin da suka goyi bayan takarar Tinubu a lokacin ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ayyana Tinubu, dan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben inda ya samu kuri’u 8,794,726.

Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu da kuri’u 6,984,520, yayin da Peter Obi na Labour Party ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.

Kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2023, APC ce ke mulki a jihohi 14 daga cikin 19 na Arewa, ciki har da Borno, Gombe da Yobe a Arewa maso Gabas, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara a Arewa maso Yamma sai Kogi, Kwara, Nasarawa da Neja a Arewa ta Tsakiya.

PDP ce ke mulki a sauran jihohi biyar: Adamawa, Bauchi, Benue, Plateau da Taraba.

‘TINUBU YA RUNGUME TARE YAFE WA GWAMNONIN AREWA’

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Tinubu ya fuskanci yanayi mai wahala a siyasance a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 amma ya ci gaba da jajircewa wajen cimma burinsa.

“Ku duka kun san cewa muna da jihohi 19 a Arewa. Daga cikin wadannan, shida ne kawai suka yi imani suka kuma goyi bayan Tinubu,” in ji Shettima.

“Banda tsohon Gwamna Abubakar Sani Bello na Neja, da ke zaune a nan, da Malam AbdurRahman AbdulRazaq… don kauce wa ce-ce-ku-ce, zan daina ambaton sunayen sauran gwamnonin.”

“Amma gwamnonin da ke goyon bayan Shugaba Tinubu a Arewa ba su wuce shida ba. Duk da haka, Tinubu ya ki karaya har sai da ya haye.”

Ya kamata darasi a siyasa ya koya wa ‘yan siyasa cewa sabani a zabe bai kamata ya raba ‘yan siyasa har abada ba.

Ya bukaci ‘yan siyasa a Kwara da su sulhunta bayan zaben fidda gwani na APC, ba tare da la’akari da wanda ya zama dan takara ba.

Mataimakin shugaban kasar ya ce Tinubu ya nuna wannan dabi’a bayan zaben 2023 ta hanyar mika hannu ga gwamnonin Arewa da ba su goyi bayan takararsa ba.

“Bayan zaben 2023, Shugaba Tinubu ya rungume su ya kuma yafe wa duk sauran gwamnonin Arewa da ba su goyi bayansa ba. Wannan alama ce ta shugaba na kwarai,” in ji shi.

Shettima ya kuma bukaci ‘yan siyasa da jami’an gwamnati da su yi aiki cikin taka tsantsan, yana mai cewa mukaman siyasa na wucin gadi ne.

“Ikona Allah ne ke bayarwa ga wadanda ya so ba don sun fi wasu mutane ba,” in ji shi.

Ya ce wadanda ke rike da mukaman gwamnati a karshe za su koma rayuwa ta yau da kullum, don haka ya kamata su yi amfani da lokacinsu a ofis wajen yi wa jama’a hidima.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma kare yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da tattalin arziki, yana mai cewa gwamnatin ta zabi magance kalubalen da ta gada maimakon bata lokaci wajen dora alhaki a kan wani.

Ya ce gwamnatin ta gaji kusan dala biliyan 3.9 a cikin asusunta kuma ta fuskanci mawuyacin halin tattalin arziki a lokacin da ta karbi mulki.

A cewar Shettima, Tinubu na ci gaba da mayar da hankali kan aiwatar da sauye-sauye duk da matsalolin da kasar ke fuskanta.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce salon siyasar shugaban ya yi tasiri ne da na marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana a matsayin dan siyasar da ba zai bari a murda masa ra’ayi ba yayin tattaunawar siyasa.

Gwamnoni da dama, shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da sauran manyan baki ne suka halarci bikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here