Gwamnatin jihar Sakkwato ta kafa wani kwamitin bincike don gano musabbabin harin da aka kai a masallacin Juma’a na Sheikh Musa Lukuwa da ke yankin Mabera a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Abubakar Bawa, ya fitar a ranar Litinin a Sakkwato.
Read also: BUK ta horar da sabbin likitocin lafiya 87 da na hakori 16
Ya ce kwamitin, wanda ya kunshi malamain addini, zai binciki abubuwan da suka haddasa tashin hankalin addini a baya-bayan nan a yankin.
Ya ce kwamitin zai bai wa gwamnati shawara kan matakan da suka dace don magance lamarin domin amfanin jihar.
“Gwamnati ta kuma bayar da umarnin rufe masallacin nan take, wanda yanzu wurin aikata laifi ne, har sai an ji sanarwa ta gaba.”
“Gwamnatin jihar ta nesanta kanta daga duk wani mutum, ko da kuwa matsayinsa, wanda ke boye a karkashin addini don raina ko rashin mutunta Annabi Muhammad, iyayensa, iyalansa da sahabbansa.”
Read also: Sports Betting Taxes: Precisely How They Work, What’s Taxabl
“Gwamnatin jihar ta sake jaddada cikakken biyayyarta da girmamawa ga Annabi Muhammad, iyayensa, iyalansa da sahabbansa,” in ji shi.
Ya bukaci mazauna jihar da su ci gaba da nuna kauna da tausayi ga Annabi.
Bawa ya yi kira ga al’ummar jihar da su guji kalaman tayar da hankali da ka iya jefa zaman lafiyar Sakkwato cikin hadari.
Ya tabbatar wa mazauna jihar kudirin gwamnati na kare rayuka da dukiyoyin kowane dan jihar.
Read also: Tinubu ya dawo Najeriya daga Landan
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa a ranar 11 ga Satumba, an yi zargin an daba wa Lukawa wuka a wuya jim kadan bayan ya jagoranci sallar Juma’a.
NAN ta ruwaito cewa masallata da ke cikin masallacin cikin fushi sun yi galaba a kan maharin tare da dukan shi har lahira nan take.












































