2027: INEC ta fitar da sunayen Yero, Shehu Sani, Katung da wasu mutum 30 a zaben Sanatocin Kaduna

Ramalan Mukhtar Yero 750x430

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da sunayen ‘yan takara 33 da za su fafata a kujerun Sanatoci  uku na Jihar Kaduna a zaben Majalisar Dokoki ta Kasa na Janairu 2027.

Jerin sunayen ya hada da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mukhtar Yero, tsohon Sanata Shehu Sani Sanata mai ci Lawal Usman da Sanata mai ci Sunday Katung.

Jerin karshe na sunayen da Sakataren Hukumar, Rose Oriaran Anthony, ta sanya wa hannu, ya nuna cewa ‘yan takara 12 za su fafata a Mazabar Kaduna ta Arewa, 13 a Kaduna ta Tsakiya da 8 a Kaduna ta Kudu.

‘Yan takarar sun fito ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban.

A Kaduna ta Arewa, an fitar Yero na APC zai fafata da Sanata mai ci Khalid na ADC.

Yero, wanda ya taba zama gwamnan jihar, na neman komawa kan mukamin da ake zaba ta hanyar Majalisar Dattawa.

A Kaduna ta Tsakiya, tsohon Sanata Shehu Sani na APC zai kalubalanci Sanata mai ci Lawal Usman na ADC.

Sani ya taba wakiltar mazabar a Majalisar Dattawa, yayin da Usman ke neman a sake zabensa.

Sauran ‘yan takarar da aka jera a Kaduna ta Tsakiya sun hada da Badamasi Hafsat ta ADP, Usman Lawal na APGA, Jatau Suleiman na APM da Ibrahim Sani na NDP.

Sauran sun hada da Bala Joji na NNPP, Adamu Haruna na NDC, Ibrahim Usman na PDP), Suleiman Babangida na PR da Salisu Suleiman na SDP.

A Kaduna ta Kudu, Sanata mai ci Katung na APC na neman a sake zaben sa da ‘yan takara da suka hada da Godfrey Gaiya na ADC, Abel Solomon na ADP da Sa’ad Abubakar na APM.

Sauran sun hada da Dauda Philibus na NNPP, Gumbari Mataimaki na PDP, Laura Lucas na SDP da Adeyemi Adebowale Abdulzeez na ZLP.

Jerin karshen ya kunshi sunan ‘yan takara, jam’iyyunsu, shekarunsu, jinsinsu da kuma cancantar da suka lissafa.

Wallafa jerin ya tabbatar da bayyana ‘yan takarar da INEC ta tantance don fafatawa a zaben Sanata na Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Tsakiya da Kaduna ta Kudu da aka shirya yi a Janairu 2027. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here