Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta wallafa jerin karshe na ‘yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu na babban zaben Janairun shekarar 2027.
Jerin, wanda Sakataren Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, aka fitar ranar Asabar a Abuja, ya kunshi ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa 18 suka tsayar domin fafatawa a kujerar.
Read also: Trade | Khám Phá Fm88 – Nơi Tận Hưởng Thế Giới Giải Trí Đỉnh Cao | 34-2025
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa rarrabar jinsi a jerin ya nuna cewa daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa 18, 16 maza ne, wanda ke wakiltar kashi 88.9%, yayin da mata 2 ne kacal.
NAN ta kuma ruwaito cewa ‘yan takarar mazan da ke cikin jerin sun hada da Bola Tinubu na APC, Abubakar Atiku na ADC da Peter Obi na NDC.
Read also: ‘Yan Bindiga sun sake kai wani sabon hari Jihar Plateau
Sauran sun hada da Adewole Adebayo na SDP, Oluseyi Makinde na APM, Donald Duke na PRP, Chibuzor Okereke na LP da Omoyele Sowore na AAC.
‘Yan takarar shugaban kasa mata kadai, wadanda suka kasance kashi 11.1% na adadin, su ne Okwori Fredrick ta NDP da Dr. Esther Okereke ta NRM.
Kididdigar jinsi na abokan takarar mataimakin shugaban kasa ma ya nuna cewa jimillar abokan takara 14 maza ne, wanda ke wakiltar kashi 77.8, yayin da mata 4 ne kacal, wanda ke wakiltar kashi 22.2 ne.
Read also: Dan gidan Kabiru Gaya ya rasu
Abokan takarar mataimakin shugaban kasa matan su ne Ofordile Egobia APP, Abubakar Usaku DLA, Konto Bintu LP da Patience Ndidi YPP.
NAN ta ruwaito cewa hukumar ta kuma fitar da jerin karshe na ‘yan takarar Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai. (NAN)












































