Dan gidan Kabiru Gaya ya rasu

IMG 20220913 WA0207 730x430 1
IMG 20220913 WA0207 730x430 1

Dan Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sadiq Kabiru Gaya ya rasu.

Sadiq, Wanda lauya ne ya rasu ne a yammacin ranar Talata a Abuja.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Solacebase, Kakakin Sanata Kabir Gaya, Hussaini Ambo Indabawa, ya ce tuni akayi jana’izar marigayin ne da misalin karfe 4:00 na yamma.

Sadiq kafin rasuwar sa, ya bar mata daya da ’ya’ya biyu.

Idan za a iya tunawa Jaridar Solacebase ta bada labarin cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, tsohon gwamnan jihar Kano, ya rasa matarsa, Halima, a watan Mayu 2020.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here