Yan Najeriya mazauna kasar amurka sun bude gidan rediyon yanar gizo a karon farko

NIDOA
NIDOA

Hadakar kungiyoyin Yan Najeriya mazauna kasar amurka (NIDOA) reshen kudancin Savannah sun kafa tarihi akaron farko na kaddamar da bude gidan rediyon yanar gizo a karon farko.

NIDOA ta yi kira ga ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da su shiga cikin shirye-shiryenta don cigaban manufofi da al’adun Najeriya.

Shugaban NIDOA na kudancin Savannah, Mista Collins Ikegwuonu ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a New York cewa za a iya sauraron rediyon ta farko ta hanyar yanar gizo a ko’ina cikin duniya.

“Wannan al’amari gaskiya ze matukar yin tasiri ga manufofin gwamnati kuma muna son kowane Najeriya ya zo ya shiga dan bada tashi gudun mawar,” in ji shi.

Ya kuma yabawa shugaban gundumar, marigayi Farfesa Joseph Igietseme, wanda ya bayar da shawarar kafa gidan rediyon kuma ya fito da wata taswirar da ayau ake aiwatarwa.

“Muna shirin gayyatar wasu ‘yan Najeriya da ke karatu a kasashen waje, musamman wadanda ke karatun aikin jarida kuma zamuyi musu abin hasafi ta hanyar samar musu da kudaden tallafi da za mu karfafa musu gwiwa don bunkasa shirye-shiryen rediyo.

Muna bukatar akalla mu sami damar tattara ‘yan Najeriya a kalla 100 a cikin kungiyar cikin kasa da shekara guda.

Ikegwuonu ya shaida wa NAN cewa tashar yanar gizon zai kasance ya karfafa gwiwar kwararrun ‘yan Najeriya da su tattauna hanyoyin baiwa matasa ‘yan Najeriya da ke shigowa Amurka dama don samun nasara kan sana’o’i masu ma’ana.

“Muna son ’yan Najeriya su fahimci cewa domin mu ba da gudummawa sosai, akwai bukatar su fara tattaunawa da mu, su kuma ba mu hadin kai dan cin gajiyar kasarmu ta haihuwa.

“‘Yan Najeriya suna da hazaka da dama kuma manyan mutane suna yin manyan ayyuka a sassa daban-daban a nan Amurka,” Ikegwuonu.

A zaben 2023, Ikegwuonu ya bukaci ‘yan Najeriya wadanda shekarun su yakai 18 da su je su samu katin zabe dan zabar Wanda ya kwanta musu aran su.

“Ya kamata a kara manhajar tsarin zabe a matsayin manhaja yayin da mutane za su san da zarar sun cika shekara 18, su mallaki katin Zaben su, su san shugabannin unguwanninsu, shugabannin kananan hukumomi, da dai sauransu.

Ya yi addu’ar Allah ya sa a yi zabe lafiya, ya kuma bukaci al’umma da su yi zabe cikin lumana ta hanyar zabar shugabanni masu nagarta, masu gaskiya, masu hankali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here