Masu ruwa da tsaki a yankin Arewa maso Yamma sun bukaci da a kafa wata doka da ta dace wadda dole ne hukumomin da abin ya shafa su biya hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Da suke ba da wannan shawara a cikin zauren bada gudummawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya shirya, sun lura cewa, hukumomi sukan dauki shekara daya zuwa biyu suna tattauna yadda za tsara shirin bada giratutin, rashin mutuntaka ne.
Masu ruwa da tsakin, wadanda akasari ma’aikatan gwamnati ne sun koka kan irin jinkirin da aka samu na biyan hakkokinsu ba tare da wani dalili ba wanda hakan ya janyo musu wahalhalu ba gaira ba dalili, wani lokutan kan kaiga mutuwar su.
Daganan masu ruwa da tsakin sun koka kan tsarin fansho na gwamnatin tarayya, babban abin da ke kawo tsaikon, shi ne rashin karbar kason da aka raba daga gwamnatin tarayya.
Don haka sun bada shawarar cewa a sake duba dokar fensho don sanya lokacin biyan kuɗi, da kuma tanadin da akai musu don kaucewa abubawan dake feuwa abaya na aikata keta lokacin biyan kuɗi.
A Kaduna, Yan fanshon Sunce sun zamo abin tausayi gameda jinkirin biyan hakkokin wadanda suka yi ritaya da kuma fansho a kasar.
Malam Abdu Magaji wanda ya yi ritaya daga aikin karamar hukumar Ja Kaduna kimanin shekaru 15, ya shaidawa Kamfanin dillacin labarai NAN cewa ya dauki kimanin watanni bakwai kafin ya karbi nasa giratutin.
Magaji wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar ’yan fansho ta Najeriya reshen karamar hukumar Soba, ya ce sai da ya shafe watanni 12 kafin a biya shi fansho, inda ya ce ya dogara ne kacokan a kan fanshonsa ne.
Farfesa Hauwau Evelyn-Yusuf, Farfesa a fannin ilimin laifuka da nazarin jinsi na Jami’ar Jihar Kaduna, ta ce wasu da suka yi ritaya sun mutu ba tare da an biya su hakkokinsu ba.
Evelyn-Yusuf, wacce kuma ita ce Babbar Darakta a cibiyar nazarin jinsi a jami’ar, ta bukaci gwamnati a dukkan matakai da su yi shirye-shiryen da suka dace don biyan ma’aikata kudadensu da zarar sun yi ritaya.
A nata bangaren, babbar sakatariyar hukumar fansho ta jihar Kaduna, Farfesa Salamatu Isah ta bayyana cewa gwamnatin jihar a halin da ake ciki nada kudaden data ke turawa ma’aikatan asusun fansho a karkashin shirin bayar da gudunmawar fansho na jihar.
Ta ce, a watan Agusta ne gwamnatin jihar ta amince da kashe Naira miliyan 860 domin biyan kudaden giratuity da na wadanda suka mutu da ma wadanda suka yi ritaya da iyalan su suka rasu.
Shima da yake bayar da gudunmuwa kan binciken, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano, Mista Kabir Ado Minjibir, ya yi kira da a gaggauta biyan hakkokin ma’aikatan gwamnati idan sun yi ritaya.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano na gudanar da wani shirin bayar da gudunmawar fansho daban da na gwamnatin tarayya dan inganta walwalar su.
Wata ma’aikaciyar gwamnati mai suna Fatima Musa da ta yi ritaya shekaru biyu da suka wuce ta ce ba a biya ta kudin giratuti ba duk da bukatar hakan da ta ke dashi..
“Ni bazawara ce; Na yi shekara biyu ina jiran in sami haƙƙina dan na sayi gida amma abin yaci tira; hakika muna shan wahala,” in ji ta.












































