Kotu ta bawa DSS dama su cigaba da rike Tukur Mamu zuwa nan da kwanaki 60

Tukur Mamu 2 750x430 2
Tukur Mamu 2 750x430 2

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, a yau Talata ta bawa DSS dama su cigaba da rike Tukur Mamu, mai sasan ce tsakanin ‘yan ta’adda da iyalan wadan da akai garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja-Kadun, zuwa nan da kwanaki 60.

Mai shara’a Nkeonye Maha ya bada umarnin ne biyo bayan lauyan hukumar tsaro ta farinkaya ya nemi da a kara musu lokaci don cigaba da binkice akan Tukur.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa ‘yan sandan Masar sun kama Tukur  Mamu tare da iyalansa a ranar 6 ga watan Satumba, ya yin da yake kan hanyar sa ta zuwa Saudiyya domin yin Umara, daga karshe suka dawo dasu gida Najeriya.

A ranar Lahadin ta gaba ta jami’an na hukumar ta DSS suka jawa ‘yan Najeiya kunne kan tufar albarkacin bakin su akan kama Tukur Mamu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here