Mutane 5 Sun Jikkata, Shaguna 17 Sun Kone Kurmus Yayin da Tukunyar Gas Ta Fashe a Jigawa

nigeria gas explosion kills at least 15
nigeria gas explosion kills at least 15

Mutane da dama sun ji raunuka daban-daban yayin da Gidajen mutane da Shaguna suka ƙone biyo bayan fashewar wata Tukunyar Gas a ƙaramar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Kakakin rundunar tsaron Sibil Defence (NSCDC) reshen jihar Jigawa, Adamu Shehu, ya tabbatar da faruwa lamarin a wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talata.

Yace lamarin ya faru ne lokacin da wata babbar Motar dakon kaya maƙare da Tukunyar Gas ta yi bindiga a Babura.

Kakakin NSCDC yace Gidaje da yawa da shagunan al’umma sun ƙone sakamakon faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa mutane da dama sun jikkata, amma har yanzu ba bu wanda ya mutu.

“Mummunan lamarin ya auku ne jiya da daddare, ranar Litinin 12 ga watan Satumba, 2022 da misalin ƙarfe 9:00 na dare,” Inji shi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here