Da Dumi-Dumi: EFCC na neman tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

Yahaya Bello, EFCC
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Hukumar EFCC ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ake nema ruwa a jallo bisa laifukan da suka shafi....

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Hukumar EFCC ta bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ake nema ruwa a jallo bisa laifukan da suka shafi tattalin arziki da kuma kudi.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis.

Karin labari AGF ta nemi tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello da ya mika kansa ga EFCC

“Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bisa laifukan da suka shafi tattalin arziki da kudi har Naira Biliyan 80.2.”

Sanarwar ta kara da cewa “Duk wanda ke da labarin inda yake to ya kai rahoto ga hukumar ko kuma ofishin ‘yan sanda mafi kusa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here