Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ta bawa kowacce jiha a Najeriya ciki harda babban birnin tarayyar Abuja tirelar shinkafa 20 domin rabawa talakawa.
Ministan yada labarai, Mohamed Idris, ne ya bayyana hakan bayan kammala taron majalisar zartaswa a ranar Litinin.
Karin labari: Kotu ta kori Dan Majalisar Wakilai a Sokoto
Ya ce kowace tirela tana ɗauke da buhun shinkafa 1,200 mai nauyin kg25 da aka ba gwamnonin jihohi a wani mataki na ragewa talakawa raɗaɗin ƙarancin abinci da tsada da ake fuskanta a ƙasar.
Haka kuma, gwamnatin tarayyar ta ce tana fatan gwamnonin jihohin za su raba kayan abincin ga mabuƙata a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.
Ana dai fama da tsadar kayan abinci da ake danganta al’amarin da matsalolin tattalin arziki wanda janye tallafin mai da matsalar tsaro suka haddasa.