Hajjin 2024: Rukunin karshe na Alhazan Najeriya sun shirya dawowa gida

Mahajjatan, Bana, hajjin, Rukunin, karshe, Alhazan, Najeriya, shirya, dawowa, gida
A safiyar ranar Talata 16 ga watan Yuli, 2024 ne rukunin karshe na mahajjatan Najeriya don gudanar da aikin hajjin 2024 zai tashi daga filin jirgin sama na...

A safiyar ranar Talata 16 ga watan Yuli, 2024 ne rukunin karshe na mahajjatan Najeriya don gudanar da aikin hajjin 2024 zai tashi daga filin jirgin sama na Sarki Abdul Azeez da ke Jeddah, wanda ke nuna nasarar kammala aikin hajjin bana.

Alhazai 312 ne daga jihar Kwara za su isa Ilorin, a cikin jirgin Air Peace. Wannan jirgin na nuni da tafiya ta 119 ta dawowa daga Saudiyya zuwa Najeriya.

A zangon farko na aikin Hajji, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta gudanar da jimillar jirage 121, wanda a yanzu an rage zuwa jirage 119 na dawowa. An dangana wannan ga iyakar amfani da kujeru yayin tafiye-tafiyen komawa.

Karin labari: Gwamnatin tarayya ta aikewa gwamnonin jihohinta tirelolin shinkafa 20

An kammala matakin dawowa kwanaki uku gabanin ranar da aka tsara tun farko na ranar 19 ga watan Yuli, 2024.

A cewar Fatima Sanda Usara, Mataimakiyar Darakta da Hukumar Jama’a na Shugaban Hukumar NAHCON, kamfanonin jiragen sama na hukumar sun dauki kwanaki 27 don jigilar dukkan alhazai zuwa Saudiyya, yayin da dawowar ta dauki kwanaki 25.

A tsawon wadannan ayyuka, an yi jigilar maniyyata 47,171 zuwa kasar Saudiyya, sannan 50,091 sun dawo Najeriya cikin wa’adi daya.

Karin labari: ’Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnoni na shirin daukar fansa

A wajen rufe taron da aka gudanar a tashar Hajji da ke Jeddah, Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya bayyana jin dadinsa bisa yadda aka kammala aikin Hajjin cikin sauki. Ya yaba da hadin kan masu ruwa da tsaki da kuma addu’o’in alhazai ga shugabanninsu.

Arabi ya bukaci maniyyatan da su ci gaba da yi wa shugabanninsu addu’a tare da kiyaye kyawawan halaye, yana mai bayyana aikin hajjin bana a matsayin alkawari da ya cika. Ya kuma bada tabbacin cewa tuni aka fara shirye-shiryen aikin hajjin 2025.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here