Yanzu-yanzu: Wani Dan Majalisar Wakilan Najeriya ya rasu

Majalisar, wakilan, Najeriya, zauna, kamfanonin, Siminti
Kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Wakilai da ke binciken hauhawar farashin siminti a kasar ya bukaci manyan masana'antar da su gabatar da takardu kan samar...

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Chikun da Kajuru a jihar Kaduna, kuma shugaban kwamitin wasanni na majalisar, Ekene Adams, ya rasu.

Dan majalisar, memban jam’iyyar Labour Party (LP), ya mutu da safiyar Talata yana da shekaru 39.

A cikin wata sanarwar mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi, ya ce dan majalisar ya kasance “ma’aikacin gwamnati mai kwazo, mai kula da wasanni, kuma mai kyautatawa”.

Ya ce Adams ya kasance “mai kirki kuma mai tausasawa, wanda duk wanda ya san shi ke so”, ya kara da cewa sadaukarwar da ya yi wajen bunkasa wasannin motsa jiki a Najeriya kuma za a yi kewar gudunmawar da ya bayar a gidan.

Karin labari: Hajjin 2024: Rukunin karshe na Alhazan Najeriya sun shirya dawowa gida

Ekene Adams

Eken Adams

Rasuwar Adams ta zo ne kasa da mako guda da rasuwar Olaide Adewale Akinremi, dan majalisar wakilai, mai wakiltar mazabar Ibadan ta arewa a karkashin jam’iyyar (APC).

Akinremi ya rasu ne makonni bayan rasuwar dan majalisar wakilai Isa Dogonyaro mai wakiltar mazabar Babura da Garki a jihar Jigawa.

Dogon yaro, ya rasu ne a watan Mayu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Karin labari: Kotu ta kori Dan Majalisar Wakilai a Sokoto

Tare da wucewar sa, Adams shi ne memba na uku a karamar majalisar da ya mutu a 2024.

Ya kasance tsohon babban manajan kungiyar kwallon kafa ta Kada City da Remo Stars, kafin ya lashe kujerar majalisar wakilai a zaben 2023.

Tsohon dan wasan kwallon kafa, Adams ya taba zama babban manajan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Remo Stars da kuma Kada City kafin ya samu kujerar majalisar wakilai a zaben 2023.

Tarihinsa na wasanni ya ba shi matsayin shugaban kwamitin wakilai kan wasanni duk da kasancewarsa na farko.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here