Kotu ta kori Dan Majalisar Wakilai a Sokoto

Majalisar, wakilan, Najeriya, zauna, kamfanonin, Siminti
Kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Wakilai da ke binciken hauhawar farashin siminti a kasar ya bukaci manyan masana'antar da su gabatar da takardu kan samar...

Kotun sauraren kararrakin zaben Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha da ke Sokoto da Zamfara da ke zamanta a Sokoto, a ranar Litinin, ta kori dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Yabo da Shagari, Umar Yusuf Yabo, wanda aka fi sani da Danmaje.

Kotun ta yanke hukuncin tare da umartar korarren dan majalisar da ya biya naira 500,000 a matsayin diyya.

Karin labari: “UAE ta dage dakatarwar shiga kasarta ga ‘yan Najeriya” – Gwamnatin Tarayya

A hukuncin da kwamitin alkalai guda uku da shugaban kotun, Mai shari’a Ashu A.Ewah ya karanta, ya bayyana zaben Danmaje a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar Yabo da Shagari a majalisar wakilai a zaman banza.

Sauran mambobin kotun sun hada da Justice Helen HammanJoda da Justice Ali Changbo.

Mai shari’a Ewah ya ce zaben da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar a shekarar 2023 da kuma sake zaben ranar 3 ga watan Fabrairun 2024 ya tabarbare da kura-kurai kamar yadda aka bayyana cikinsa.

Karin labari: ’Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnoni na shirin daukar fansa

Kotun ta kuma umarci INEC da ta shirya tare da gudanar da wani zabe a cikin kwanaki 90 masu zuwa daga yau.

Za a gudanar da zaben ne a mazabu biyu da abin ya shafa na karamar hukumar Shagari

Kotun dai ta umarci INEC da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Danmaje tare da gudanar da zaben a wuraren da abin ya shafa cikin kwanaki 90.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here