Najeriya ta yi asarar Naira Tiriliyan 2.2 saboda biyan kudaden fansa ga masu garkuwa cikin shekara ɗaya – Rahoto

Gunmen

Kungiyar da ke rashin tabbatar da adalci da daidaito a ayyukan gwamnati (CISLAC) tare da kungiyar tabbatar da adalci ta (TI) Najeriya sun fitar da rahoton su na takwas kan manufofin cigaban ƙarni mai ɗorewa (SDG 16), inda suka bayyana cewa tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024, Najeriya ta yi asarar sama da Naira tiriliyan 2.2 sakamakon biyan kudaden fansa ga masu garkuwa da mutane.

Wannan adadi, a cewar rahoton, ya fi dukkan kasafin kudin tsaron ƙasar na shekarar 2024

Rahoton Mai taken “Kada a Bar Kowa a Baya: Yaki da Cin Hanci, ‘Yancin Samun Bayani, da Adalci ga Kowa da Kowa.” an ƙaddamar da shi a wani taron gefen babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar a birnin New York.

A wajen taron, shugaban CISLAC kuma shugaban (TI) a Najeriya, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani), ya bayyana damuwa cewa Najeriya na cikin mummunan yanayi na cin hanci, raunin hukumomi da ƙara tabarbarewar tsaro, abin da ka iya hana ta cimma manufofin cigaban ɗorewa na 2030.

Rafsanjani ya ce daya daga cikin abubuwan da suka fi tayar da hankali a rahoton shi ne yawaitar garkuwa da mutane wanda ya zama tamkar kasuwanci.

Ya bayyana cewa sama da mutum miliyan 2.23 aka yi garkuwa da su a cikin watanni 12, inda kudaden fansar da aka biya suka kai Naira tiriliyan 2.2, kwatankwacin dala biliyan 1.4.

Wannan ya nuna yadda tsaro ya koma hannun masu zaman kansu a kan farashin zaman lafiyar ƙasa.

Ya ƙara da cewa rashin bin doka da ‘yan siyasa ke yi shi ne tushen gazawar mulki a Najeriya, musamman kin bayyana kadarorinsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Wannan, a cewarsa, yana ƙara karya amincewar jama’a ga gwamnati tare da hana hukumomin yaki da cin hanci yin aikinsu yadda ya kamata.

Haka kuma ya zargi shugabanni da karkatar da kuɗaɗen haraji don siyan manyan gidaje a Najeriya da ƙasashen waje, abin da ke ƙara ƙarfafa safarar kuɗaɗen haram.

Rahoton ya kuma yi gargadi kan rashin gaskiya a batun dawo da kadarorin sata, yana nuna cewa ana yin hakan ba tare da bayani ko cikakken lissafi ba.

Har ila yau, ya nuna raunin hukumomin da ya kamata su kare dimokuraɗiyya, ciki har da kotuna, hukumar zaɓe da hukumomin tsaro, waɗanda jama’a ke kallon sun lalace saboda matsin lamba daga masu mulki.

Daga cikin misalan da rahoton ya kawo akwai kama wani matashi mai fallasa badala a Jihar Katsina, Mubarak Bello, bayan ya tona asirin almundahana a hukumar ‘yan sanda ta jihar.

Haka kuma ya ambaci shari’o’in kadarori da suka shafi manyan ‘yan siyasa da lauyoyi, ciki har da zargin kadarorin da ake danganta da Ministan Abuja, Nyesom Wike, a Florida, Amurka.

A ƙarshe, Rafsanjani ya bayyana rahoton a matsayin madubi da kuma taswira, yana mai kira da a sake sabunta jajircewa wajen aiwatar da nagartaccen mulki.

Ya ce hanya guda da za ta ceto Najeriya daga tabarbarewar ita ce ƙarfafa hukumomi, kare ‘yancin jama’a da mutunta doka da oda, domin kawai hakan zai tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here