Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa kan wata talla ta bogi da aka kirkira ta hanyar fasahar (AI), wadda ke yawo a dandalin Facebook da ke amfani da hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
An bayyana cewa tallar ta yi ƙarya tana ikirarin jawo mutane su zuba jari a cikin wani tsarin zamba na Ponzi scheme.
A cewar gwamnatin tarayya, ba Shugaban ƙasa ba ne ya amince da tallar, kuma ba ta wuce ofishin hukumar kula da talla ta Ƙasa (ARCON) ba, wadda ke ƙarƙashin ma’aikatar bayar da bayani da kula da Al’adu.
Hukumar ta ce an saba dokokin talla na 2022, abin da zai iya jawo hukunci ga masu hannu a ciki.
Daraktan ARCON, Dakta Olalekan Fadolapo, ya fitar da sanarwa inda ya yi gargadi cewa jama’a su yi hattara, domin tallar bogi ce da ta yi amfani da hotuna da bidiyon Shugaba Tinubu wajen neman kuɗin mutane.
Ya ce irin wannan yaudara na iya jawo barna da ɓata sunan gwamnati.
Hukumar ta kuma yi kira ga masu gidan jarida da jama’a su kasance masu lura, tare da tabbatar da cewa ba su bayar da dama ga irin waɗannan tallace-tallace marasa tushe ba.
Haka kuma ta jaddada cewa duk wani tallan da ba a kai ofishinta don tantancewa ba, ba shi da inganci kuma haramun ne.
Rahoton ya kuma tuna da wasu irin tallace-tallace da aka taba kirkirawa da hotuna da muryar kwamfuta na fitattun mutane irin su Fasto Enoch Adeboye da dan jarida Seun Okinbaloye, inda aka yi amfani da su wajen yaudarar jama’a da magungunan bogi da kuma dabarun satar kuɗi.
A ƙarshe, ARCON ta jaddada aniyar ta na samar da tsarin talla na gaskiya da ke kare masu amfani, tare da kira ga masu ruwa da tsaki su kiyaye ƙa’idojin gaskiya da amana wajen tallata kayayyaki da ayyuka.













































