Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Kwara, Dakta Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana matukar alhininsa game da kisan gillar da aka yi wa Hafsoh Lawal, dalibar Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara, wanda ake zargin Abdulrahman Bello, wani fitaccen malamin addinin Musulunci ya kashe ta.
Sarkin ya umurci Limamai a fadin jihar da su rika amfani da hudubar Juma’ar da suke yi wajen nuna illar yaki da kashe-kashe da sauran munanan ayyuka, inda ya jaddada wajabcin kiyaye kyawawan halaye da mutunci a cikin al’umma.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mallam Abdulazeez Arowona ya fitar a ranar Lahadi, Sulu-Gambari ya yi Allah wadai da lamarin, yana mai bayyana lamarin a matsayin “abin takaici, wanda ya saba wa al’adar Ilorin.
Sarkin a cikin sanarwar ya kara jaddada cewa aiki tukuru ne kadai ke samun nasara, inda ya yi kira da a yi yaki da zaman banza, lalaci, da zage-zage da matasa ke yi ba tare da wani dalili ba.
Karanta: Yadda sarkin Ilorin ya dauki nauyin karatun Hadiminsa daga matakin Firamare zuwa Jami’a
Sarkin ya kuma bukaci malamai a masarautar Ilorin da sauran su da su taimaka wajen zakulo mutane irin su Abdulrahman Bello ga hukumomin tabbatar da doka da oda a kan su.
Da yake jajantawa iyalan marigayiya Hafsoh Lawal, Sulu-Gambari ya yi kira ga ‘yan sandan Najeriya da bangaren shari’a da su tabbatar an yi adalci.
Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wani malamin addinin Islama mai shekaru 29 a duniya bisa zargin kisan Hafsoh Lawal a ranar Talata, 11 ga watan Fabrairun 2025, wanda ake zargin sun hadu da ita a Facebook.
Wanda ake zargin, wanda kuma malamin addinin Islama ne, an yi zargin cewa ya gayyaci yarinyar ne ta hanyar wayar tarho a ranar Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025, kuma daga bisani ya kashe ta tare da boye ta ta a wani wuri a unguwar Olunlade da ke wajen garin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa an fara gudanar da bincike.












































