Sojojin Nijeriya da DSS sun kara kama mutum 2 da ake zargi da kai harin cocin Owo a jihar Ondo  

owo killing
owo killing

Shelkwatar tsaro ta bayyana cewa ta samu nasarar kara cafke ‘yan ta’addan da suka kai hari a cocin St. Francis Catholic Church da ke garin Owo, a jihar Ondo.

Darkatan yada labarai na hukumar, Jimmy Akpor, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis.

Sanarwa ta ce ankama wadan da ake zargin ne a Omialafara, Ose, da ke jihar Ondo.

Akpor ya ce kaman nasu anyi shine sa’o’i kadan bayan kama wasu mutane hudu wa dan da suma ake zargin su da hannu dumu dumu wajan kai harin.

Ya kara da cewa an sami nasar kaman ne bisa hadin gwaiwa da rundunar sojoji da kuma jami’an tsaro na farin kaya ta DSS. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here