‘Yan sanda sun tsairatar da masu damfara 3 daga hannun masu daukar doka a hannu a Abuja

Nigeria Police Constable Recruitment
Nigeria Police Constable Recruitment

Jami’an ‘yan sanda a Abuja sun sami nasarar kobutar da wasu mutane uku da ake zargin su da damfara ta hanyar yanar gizo daga hannun wasu fusatattun mutane masu daukar doka a hannu a unguwar Lokogoma da ke cikin Abuja.

Maimagana da yawun hukumar ‘yan sadan Abuja, Josephine Adeh, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar yau Alhamis a garin Abuja.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan Abuja, Mista Babaji Sunday, ya ja hankalin jama’a da su gujewa daukar doka a hannu su.

Ya ce binkicen ‘yan sandan ya bayyana cewa wadan da ake zargin sunyi yunkurin damfarar wata mata mai sana’ar POS, wanda hakan ya fusata mutanan.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce sakamakon shiga lamarin da suka yi, yanzu haka wanda ake zargin suna hannun hukumar.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here