Wata kotu ta bada umarnin tsare wata budurwa mai suna Olufumilayo Brioluwa a gidan yari na Kirikiri bisa laifin cin zarafin wani dan sandan Najeriya a jihar Legas.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wani sakon Twitter da ya wallafa.
A cewar Hundeyin, Brioluwa ya farwa dan sandan ne a yankin Ogombo da ke jihar.
Ana ci gaba da tsare ta a gidan gyaran hali na Kirikiri har zuwa ranar 6 ga watan Yuni lokacin da za a kaita kotu.













































