Manoma da Makiyaya sun cimma matsayar samar da zaman lafiya a Katsina

Manoma, Makiyaya, cimma, matsayar, samar, zaman, lafiya, Katsina
Manoma da makiyaya a karamar hukumar Kankara (LGA) ta jihar Katsina sun amince da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummarsu ta hanyar tattaunawa...

Manoma da makiyaya a karamar hukumar Kankara (LGA) ta jihar Katsina sun amince da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummarsu ta hanyar tattaunawa.

Kungiyoyin sun amince da kawo karshen rikicin da aka dade ana gwabzawa tsakanin manoma da makiyaya, a wani taron tattaunawa na al’umma a Kankara ranar Alhamis.

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Mercy Corps tare da hadin gwiwar kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM) da cibiyar dimokaradiyya da ci gaban kasa (CDD) ne suka shirya taron da nufin bunkasa ayyukan noma a yankunansu.

Karin labari: Kwalara: Hukumar NAFDAC ta sanya idanu kan masu saida abinci a Sokoto

An shirya shi ne a karkashin shirin wata kungiya tare da tallafin kudade daga Tarayyar Turai (EU).

A cewar shugabannin manoma da makiyaya na yankin Kankara da Ketare na karamar hukumar, sun cimma yarjejeniyar ne domin amfanin al’ummarsu da kuma ci gaban kasa.

Sun kara da cewa yarjejeniyar ta zama dole, duba da cewa idan babu zaman lafiya ba za a samu ci gaba a yankunansu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here