Gobara ta tashi a Fadar Sarkin Kano ta Kofar Kudu

1720890867569

Wata gobara da ake zargin wasu da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba suka kunta ta tashi tare da lalata wani bangare na fadar Gidan Rumfa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 16 ke zaune.

Lamarin dai kamar yadda majiya daga fadar ta bayyana, ta ce lamarin ya faru ne a daren Juma’a da misalin karfe 11 na dare.

Majiyar ta ce daya daga cikin manyan fadan da ke Kofar Kudu inda Sarkin ke zama ta samu matsala sosai.

“Fadar Kofar Kudu ce. Ka san fadar tana da mashiga daga ciki yayin da babbar kofar daga gaba take (waje). Makullin da karfi aka bude shi, abin da ake zargin shi ne wasu ne suka kunna wutar, sannan suka kulle kofar.”

Majiyar ta ce “An lalata gadon sarauta, na’urorin sanyaya daki da sauran kayayyaki masu daraja a fadar.

Da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ce rundunar ba ta da labarin faruwar lamarin domin babu wani kira dangane da faruwar lamarin a duk wata cibiya ta hukumar.

Sai dai a wata sanarwa da shugaban ma’aikatan fadar Sarkin Kano, Munir Sanusi Bayero, Dan Buram Kano ya fitar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “A ranar Asabar, 13 ga Yuli, 2024 da safe, gobara ta tashi a farfajiyar wajen fadar mai martaba, Kofar Kudu. Abin farin ciki, ba a sami asarar rai ba, kuma barnar ba ta da yawa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here