
Rahotanni sun ce ‘yan ta’addar Boko Haram sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Jakana da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno a ranar Lahadi.
Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar direban dan sanda da wata mata, haka zalika sun kona motocin sintiri guda biyu na ‘yan sanda da na Civilian Joint Task Force (CJTF).
SolaceBase ta bayyana cewa sun kuma yi amfani da makamai da alburusai da dama.
Jakana, mai tazarar kilomita 45 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno ce, tare da babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, an kai harin da sanyin safiyar yau.
Karin labari: An kama wasu Ma’aurata da suka sayi Jariri daga hannun mai fataucin Yara yayin bikin radin Suna
‘Yan ta’addan sun isa ne da safe inda suka yi artabu da ‘yan sanda kusan sa’o’i uku. Daga karshe ‘yan tada kayar bayan sun ci karfin jami’an tsaron inda suka gudu da nisan mil 3.
Shugaban karamar hukumar Konduga Abbas Ali Abari ya tabbatar da faruwar lamarin.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Borno ba ta bayar da cikakken bayani kan lamarin ba.
Karin bayani na tafe…