An kama wasu Ma’aurata da suka sayi Jariri daga hannun mai fataucin Yara yayin bikin radin Suna

'Yan sanda, kama, wasu, Ma'aurata, mata, miji, sayi, Jariri, hannun, fataucin, Yara yayin, bikin, radin, Suna
Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ceto wani jariri dan watanni biyu daga hannun wasu ma’aurata miji da mata, James Uwam, yayin bikin radin sunan shi...

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ceto wani jariri dan watanni biyu daga hannun wasu ma’aurata miji da mata, James Uwam, yayin bikin radin sunan shi.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar a ranar Asabar, ta ce ma’auratan sun biya zunzurutun kudi har Naira miliyan 2,350,000 don siyan jaririn daga hannun wani da ake zargin mai fataucin yara ne mai suna Loretta Nelson, wanda ya sayi jaririn a hannun wani Fasto mai suna Peter Udoh a kan kudi Naira 1,450,000.

Sanarwar ta ce Udoh ya sayi jaririn ne a kan kudi Naira 500,000 daga hannun wata mai suna Gloria Sunday da ake zargi da satar jaririn a ranar 11 ga watan Yuli, 2024, lamarin da ya sa mahaifiyar jaririn ta kai kara zuwa ga hukumar ‘yan sanda.

Karin labari: “Yadda Tinubu Zai Hana Zanga-zanga” – Kungiyar Goyon Bayan Atiku

Bayan rahoton, sanarwar ta ce ‘yan sanda sun zage dantse ne a ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya kai su ga cafke wasu da ake zargi da aikata laifin da jami’an ‘yan sanda na sashin Oko Oba na rundunar ‘yan sanda suka yi.

Kakakin ya ce, “Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin kama Gloria Sunday wacce a lokacin da ake yi mata tambayoyi ta ce ta sayar da jaririyar a kan N500,000 ga wani Fasto Peter Udoh.

Fasto Udoh, wanda daga baya aka kama shi a garin Ikene na jihar Ogun, ya amince ya sayar da yaron kan kudi N1,450,000 ga wata Loretta Nelson da aka kama a Festac Town a Legas.

Karin labari: Rushewar Gini: ‘Yan Sanda a Jigawa sun tabbatar da mutuwar wasu Leburori 3

Ya ce Nelson ya amsa laifin sayar da jaririn a kan Naira miliyan 2,350, ga wasu mata da miji Mista da Misis James Uwam da aka kama a lokacin bikin radin sunan yaron da aka sace.

Sanarwar ta ce an fara bincike kuma za’a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here