Yana da kyau mahukunta su mai da hankali wajan bunkasa binciken noma da kiwo – Farfesa Salisu Shehu

IMG 20230408 WA0009
IMG 20230408 WA0009

Shugaban jami’ar Al-istiqama dake sumaila a jihar kano, Farfesa Salisu Shehu, ya yi kira ga mahukunta da su maid a hankali wajan bunkasa cibiyoyin binciken noma da kiwo, domin samar da wadatatcen anbinci ga al’umma.

Shehu yayi wannan kiran ne yayin gudanar da taron laccar Azumin watan Ramadan, karo na bakwai, wanda kungiyar Inuwar Musulmin Najeriya ta shirya ranar asabar a Kano.
“Yadda muka wadatu da ilimin kimiyya da fasaha, bai kamata ace muna zaune yunwa tana neman hallaka mu ba, ya kamata mu kara kaimi wajen bawa noma da kiwo muhimmanci.”

“Yunwa tai mana katutu a kasar nan, yana da kyau mu samu hadin kan masu ruwa da tsaki a harkar noma da kiwo domin kawo sauyi a cikin al’umma.”
Shehu wanda shine ya wakilci shugaban kungiyar, Janar Ahmad Muhammad Daku, ya kara da cewa al-umma suma sunada gunmawar das u bayar wajan kawo sauyi a al-amuran da suka shafi yau da kullum.
“Ya kamata mutane suma su dunga bada gudun mawar su a bangarori da dama, bai kawai a zubawa gwamnati ido ba.”

Injiniya Muhammad Lawan Maidoki, wanda na daya daga cikin wadanda suka gabatar da lacca a gurin taron, shima ya ja hankalin mahukunta dasu mai da hankali wajan kulawa da madatsan ruwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here