Rushewar Gini: ‘Yan Sanda a Jigawa sun tabbatar da mutuwar wasu Leburori 3

Rushewar, Gini, 'Yan Sanda, Jigawa, tabbatar, mutuwar, wasu, Leburori
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu leburori uku a wani gini da ya rufta a karamar hukumar Taura ta jihar. Jami’in hulda da...

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu leburori uku a wani gini da ya rufta a karamar hukumar Taura ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shisu, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a Dutse.

Shisu ya lura cewa ‘yan sanda sun samu labarin lamarin da misalin karfe 10 na safe lokacin da lamarin ya faru a ranar Asabar a garin Gujungu da ke karamar hukumar Taura.

Ya bayyana cewa da samun rahoton, tawagar ‘yan sanda ta garzaya wurin da lamarin ya faru.

Karin labari: Zanga-zanga: ‘Yan Kasuwa A Kano Sun Samar Da Matakan Tsaro Don Kare Kasuwannin Su

Hukumar ta kara da cewa isar tawagar ta gano cewa wani gini ne mai hawa biyu da ake ginawa ya ruguje.

Ya kara da cewa, a sakamakon lamarin, mutane uku ne suka mutu a nan take, yayin da wasu hudu suka samu raunuka daban-daban.

A cewarsa wadanda suka rasa rayukansu a lamarin sun hada da; Nafi’u Mohd mai shekaru 28 mazaunin unguwar Rijiyar Zaki a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano sai Abdurrahman Ibrahim mai shekaru 60 da Usaman Lawan Muhammad mai shekaru 62, dukkansu mazauna kauyen Danmadai da ke karamar hukumar Gagarawa na jihar Jigawa ne.

Karin labari: ‘Yan Majalisar Wakilai a Najeriya na dab da cirewa Jami’o’in Tarayya kudin wutar lantarki

Shisu ya lissafa wadanda suka jikkata kamar haka; Umar Lawan mai shekaru 26 da Aminu Mohd mai shekaru 25 sai Mudansir Nasiru mai shekaru 26 da Usman Mohd mai shekaru 20, duk ‘yan Rijiyar Zaki ne a yankin Karamar Hukumar Ungogo a jihar Kano.

Ya kara da cewa duka gawarwakin da wadanda abin ya shafa an garzaya da su babban asibitin Jahun domin duba lafiyarsu, yayin da binciken farko ya nuna cewa wadanda abin ya shafa leburori ne da ke aikin ginin.

“A bisa haka, kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP A.T Abdullahi, ya jajantawa iyalan mamatan tare da addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.” Inji kakakin rundunar kamar yadda NAN ta wallafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here