Gwamnatin Tarayya ta bayyana wa’adin kammala ayyukan titin Abuja, Kaduna, Zaria da Kano

Gwamnatin, Tarayya, bayyana,, wa'adin, kammala, ayyukan, titin, Abuja, Kaduna, Zaria, Kano
Gwamnatin Tarayya ta ce za a kammala ayyukan titin Abuja da Kaduna da Zaria da kuma Kano a ranar 29 ga watan Mayu, 2025. Ministan ayyuka David Umahi ne ya...

Gwamnatin Tarayya ta ce za a kammala ayyukan titin Abuja da Kaduna da Zaria da kuma Kano a ranar 29 ga watan Mayu, 2025.

Ministan ayyuka David Umahi ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da aikin titin Abuja da Kaduna da kuma Zaria da Kano a ranar Asabar a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

NAN ta rawaito cewa taron ya kuma shaida kaddamar da shirin “Operation Free Our Roads” da nufin tabbatar da ganin an samu dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya.

Umahi ya kara da cewa, taron kuma shi ne mika sashin titin mota mai tsawon kilomita 38 ga rukunin kamfanonin Dangote da kuma kaddamar da aikin “Operation Free Our Roads”.

Karin labari: Rushewar Gini: ‘Yan Sanda a Jigawa sun tabbatar da mutuwar wasu Leburori 3

Ya bayyana cewa kamfanonin gine-gine uku ne za su kammala aikin hanyar wadanda suka hada da: Dangote da Julius Berger da kuma BUA.

“An fara aikin ne da gyaran fuska kawai a karkashin gwamnatin da ta shude akan Naira biliyan 155 daga baya kuma aka fadada aikin kuma aka kara farashin zuwa Naira biliyan 655.

“Lokacin da muka hau jirgin a watan Satumbar bara Julius Berger ya nemi a sake duba farashin Naira Tiriliyan 1.5 kuma anan aka fara dambarwar.

“Duk da haka, mun samu damar yadda, sannan kuma mun samu mai ba da shawara mai zaman kansa, wanda ya sake duba aikin tsakanin Berger da Ma’aikatar Ayyuka kuma kusan watanni tara kenan,” in ji shi.

Karin labari: Zanga-zanga: ‘Yan Kasuwa A Kano Sun Samar Da Matakan Tsaro Don Kare Kasuwannin Su

Umahi ya ce an duba kudin aikin zuwa kusan Naira biliyan 888 tare da banbancin biliyan 640 daga abin da Berger ke bukata domin hada titin mai hawa uku.

Ya ce Berger za su kammala sashinsu na hanyar da ke da nisan kilomita 82 akan kusan Naira biliyan 320.

Ya kara da cewa bangaren Dangote wanda ke da nisan kilomita 38, zai ci Naira biliyan 126, yayin da bangaren BUA mai nisan kilomita 8.66 sau biyu zai ci Naira biliyan 41.9, in ji Umahi kamar yadda NAN ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here