
Kungiyar matasan Najeriya na Atiku Abubakar (NYFA), mai goyon bayan burin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ta ce shugaban kasa Bola Tinubu na iya yin jawabi ga al’ummar kasar tare da sauya wasu manufofi don rage barazanar zanga-zanga.
Shugaban NYFA, Farfesa Gold Emmanuel ne ya bayyana haka a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na kungiyar Mista Dare Dada ya sanyawa hannu ranar Asabar a Legas.
Emmanuel ya ce duk da haka ‘yan Najeriya na da damar gudanar da zanga-zangar adawa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya kuma dorawa gwamnati alhakin kare masu zanga-zangar daga duk wani nau’i na hare-hare da kutsawar bata gari.
Karin labari: Gwamnatin Tarayya ta bayyana wa’adin kammala ayyukan titin Abuja, Kaduna, Zaria da Kano
Shugaban NYFA ya kara da cewa: “Ba labari bane cewa a halin yanzu ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.
“Ya kamata gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yiwa kasar jawabi a wannan mawuyacin lokaci, maimakon rufe bakin mutane.
“Wannan ba al’ada ba ce a kowace kasa mai ci gaba inda dimokuradiyya ke mulki.
“Mayar da duk wasu manufofin kyamar mutane a Najeriya kuma ya zama dole a cikin kiraye-kirayen gudanar da zanga-zanga a fadin kasar,” in ji Emmanuel.
A cewarsa, gwamnati ba za ta wanzu ba tare da jama’a ba, don haka dole ne a mutunta ‘yan kasa.
Karin labari: Zanga-zanga: ‘Yan Kasuwa A Kano Sun Samar Da Matakan Tsaro Don Kare Kasuwannin Su
“Dole ne mu taka a hankali kuma mu saurari mutanen da muke wakilta,” in ji sanarwar.
Emmanuel, ya bukaci masu son yin zanga-zangar da su gudanar da rayuwarsu cikin lumana ba tare da yin tashin hankali ba.
“Muna kira da shugaban kasa da ya umarci dukkan hukumomin tsaro da su kare su ta yadda baza a samu rasa rayuka ba.”
Shugaban NYFA ya shawarci shugaban kasa da ya binciki damuwar dan kasuwar Najeriya kuma shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, game da bangaren Man Fetur.
Karin labari: Rushewar Gini: ‘Yan Sanda a Jigawa sun tabbatar da mutuwar wasu Leburori 3
Farfesan ya ce dole ne Shugaba Tinubu ya kasance mai burin kawowa al’ummarsa da suka dade suna fama da ci gaba ta hanyar daukar wannan alkawari da gaske, ba wai alkawarin jeka nayi ka ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kungiyar NYFA ta zabi goyon bayan Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 ne, tare da kara masa kwarin gwiwa da ya sake ba ta dama a 2027.
An samu rahotannin cewa wasu ‘yan Najeriya a karkashin hukumomi daban-daban na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar daga ranar 1 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Agusta, kan tsadar rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki kamar yadda NAN ta wallafa.