A ranar juma’an nan ne ya yin da babbar kotun gwamnatin tarayya da take gudanar da shara’ar Tukur Mamu a Abuja, ta umarci yan jaridu da lauyoyi da su fita daga cikin Kotun.
Lauya Kaswe ne ya rako mai shara’a Inyang Ekwo da ya bada umarnin duk yan jaridu da lauyoyi su fita daga zauren kotun.
“Ina rokun wannan kotun mai albarka data bada umarni duk wanda wannan shara’ar bata shafe shi ba ya fita daga cikin kotun nan.”
Mai shara’ar ya karbe rokun da lauyan ya yi, inda ya umarci duk wani lauya wanda bada shi ake shara’ar ba ko kuma yan jaridu da duk wanda shara’ar bata shafe shi ba da ya fice daga zauren kotun.
Tukur Mamu dai na fuskantar shara’ar da gwamnatin taryya ke zargin sa da hada hannu da yan ta’adda a kasar nan.