NCAA ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin gurbacewar man jirgi

NCAA
NCAA

Hukumar dake kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Ƙasa, NCAA ta fara gudanar da bincike domin gano dalilin gurbacewar man jirgi da aka samu a yan kwana kin nan, domin kiyaye kara faruwar lamarin anan gaba.

Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa an dakatar da kamfanin jirgin sama na Max Air sakamakon amfani da gurbatatcen mai jirgi da ya yi  a wani jirgi mallakin sa da ya taso daga Yola zuwa Abuja.

Ya yin da yake magana a gurin taron da yai da kamfanonin jiragen sama masu zirga zirga a cikin gida, da kuma kamfanoni masu sayar da man jirgi, shugaban hukumar NCAA Kaftin Musa Nuhu ya ce hukumar tasa ta fara bincike domin gano musabbabin faruwar matsalar tun daga tushe domin magance ta.

Ya kara da cewa dole ne a hada hannu da masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here