Kotun kolin masana’antu ta kasa (NIC), ta umurci kamfanin BUA Flour Mills, da ya biya ma’aikatanta 11 da suka kora daga aiki.
Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Ebeye Isele, ya bayar da umarnin a biya biyar daga cikin wadanda masu karar, Aliyu Kabara, Idris Isah, Abdullahi Mohammed, Mohammed Abdullahi da Ahmed Mohammed, jimillar Naira miliyan 1.4, N261,360, N216,000, N261. ,000 da kuma N522,720, a matsayin kudaden sallama.
Kotun ta kuma umurci wanda ake kara da ya biya sauran mutane 6 da suka rage, Rabiu Hamisu, Lawan Sanusi, Salisu Garba, Valentine Watsav, Yusuf Usman da Augustine Clement, wadanda suka kwashe kasa da shekaru biyar suna aikinsu na albashin wata guda.
NIC ta jaddada cewa dole ne a biya dukkan kudaden a cikin wata daya da yanke hukuncin.













































