Jihar Borno ta tabbatar da cewa ISWAP ta sace ma’aikacin lafiya

D1E76E1D 5299 4D03 AA95 67AD3BBFEBD4
D1E76E1D 5299 4D03 AA95 67AD3BBFEBD4

Gwamnatin Borno a ranar Laraba ta tabbatar da sace wani ma’aikacin lafiya da ke babban asibitin Gubio, Mista Bulama Geidam, da kungiyar Islamic State of West African Province (ISWAP) ta yi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa mayakan ISWAP sun kai hari garin Gubio a ranar Laraba da misalin karfe biyu na rana tare da wawashe kayan abinci da mai daga wata motar jin kai.

Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Juliana Bitruce, wacce ta tabbatar wa NAN da yin garkuwa da shi a Maiduguri, ta ce lamarin “abin takaici ne kuma mai tayar da hankali”.

Ta ce ma’aikacin lafiya da aka sace na daga cikin wadanda suka ci gaba da zama a bakin aikinsu duk da kalubalen rashin tsaro a yankin.

NAN ta ruwaito cewa mazauna garin da suka gudu domin tsira a lokacin harin sun koma gidajensu bayan da maharan suka janye daga garin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here