Saudiya ta sa ranar Asabar 13 ga wata Agusta a matsayin ranar da za’a gama kwashe alhazan da suka gudanar da aikin Hajjin bana daga kasar baki daya.
Hukumar dake kula da aikin Hajji da Umara da kasar ta ce kamfanonin jiragan da sukayi jigilar alhazan dole su gama kwashe alhazan daganan zuwa wa’adin da aka basu.













































