Hukumar da ke kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta kasa (NCoS), ta ce zata hada gwaiwa da sauran jami’an tsaro domin bin sahun wadan da suka tsaire daga gidan yarin Kuje da kuma sauran gidajen yari a fadin kasa baki daya.
kakakin hukumar na kasa, Mista Abubakar Umar, ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hakan yau Alhamis a Abuja.
Ya ce hakan na da mutukar anfani idon hukumomin tsaro suka yi aiki tari don magance matsalar tsaro da ke damun Najeriya.
Umar ya ce hukumomin tsaro kamar ‘yan sanda, sojoji da kuma sauran jami’an tsaro na bada gudun mawa sosai ga hukumar ta NCoS.
Ya kuma kara da cewa babban kwanturola na hukumar ta NCoS, ya bada umarni ga jami’an na hadin gwaiwa da su fara hada duk wani bayanai da zai taimaka wajan kara kama wadan suka tsire.













































