Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin shugabannin rundunonin tsaro da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar domin amincewa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa waɗanda aka tabbatar sun haɗa da Janar Olufemi Oluyede a matsayin shugaban ma’aikatan tsaro, Manjo Janar Waheedi Shaibu a matsayin shugaban rundunar sojojin ƙasa, Mataimakin Marshal Kennedy Aneke a matsayin shugaban rundunar sojin sama, da kuma Rear Admiral Idi Abbas a matsayin shugaban rundunar sojin ruwa.
Idan za a iya tunawa shugaban ƙasa Tinubu ya tura wasiƙa ga shugaban majalisar dattawa a ranar 27 ga Oktoba don neman a duba bukatar da gaggawa tare da tabbatar da nadin sabbin shugabannin tsaron.
Ya ce wannan mataki na cikin tsarin sake fasalin tsaro don ƙarfafa ƙwarewa, haɓaka haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kuma ƙara wa jami’an tsaro ƙwarin gwiwa.
A lokacin tantancewa, shugaban rundunar sojin ruwa, Rear Admiral Idi Abbas, ya bayyana cewa rundunar za ta yi amfani da fasahar zamani, musamman jirage marasa matuka wato ɗron, don ƙarfafa tsaron ruwa da rage laifukan da ake aikatawa a cikin hanyoyin ruwa na ƙasar.
Ya ƙara da cewa rundunar na da tsarin aiki, amma amfani da fasahar zamani zai taimaka wajen rage kuɗi da ƙara inganci.
Haka kuma Abbas ya ce an kafa rundunar ayyuka ta musamman a Makurdi, Jihar Benue, domin ƙarfafa sintiri da aikin kai dauki tsakanin yankin Benue da Lokoja.
Ya kuma bayyana cewa babu buƙatar ƙirƙirar sabuwar hukumar Coast Guard, domin rundunar sojin ruwa ta riga tana yin ayyukan irin na wannan hukumar.
Shugaban rundunar tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana lokacin da yake shugabantar rundunar sojin ƙasa a matsayin lokaci mai wahala amma mai cike da nasara, inda ya bayyana bukatar haɗin kai daga kowane ɗan Najeriya domin tabbatar da tsaron ƙasa.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Jibrin Barau, ya bukaci sabbin shugabannin tsaron da su kasance masu biyayya ga shugaban ƙasa da kundin tsarin mulki, yayin da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tantancewar ta zama wajibi don tabbatar da cewa ƙwararru da masu kishin ƙasa ne kaɗai za su jagoranci harkokin tsaro.
NAN