Jami’an hukumar JAMB sun fice daga zaman Majalisar Wakilai saboda halartar ’yan jarida

Reps new 750x430 (1)

Jami’an hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) sun fice daga zaman kwamitin Majalisar Wakilai da aka gudanar a Abuja, bayan sun ƙi yarda da kasancewar ’yan jarida a wurin.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa zaman an shirya shi ne domin duba yadda aka gudanar da kasafin kuɗin shekarar 2023/2024 da kuma yadda hukumar ta JAMB ta tafiyar da kuɗaɗenta.

Jagoran tawagar JAMB, Mufutau Bello, wanda darakta ne a hukumar, ya nemi a gudanar da zaman ne a sirri, amma ya samu sabani da kwamitin bisa kasancewar ’yan jarida a wurin, lamarin da ya sa shi tare da sauran mambobin tawagarsa suka fice daga zaman.

Shugaban kwamitin, Oboku Oforji daga jihar Bayelsa, ya bayyana cewa wannan mataki na tawagar JAMB abin takaici ne kuma ba zai karbu ba, yana mai cewa Majalisar ba za ta lamunci duk wani yunƙurin raina ikon ta na sa ido kan hukumomi ba.

Ya ce kwamitin ya aike da wasiku uku a jere zuwa ga babban sakataren JAMB, yana neman takardun bayanin yadda aka kashe kasafin kuɗi, bayanan asusu, da hujjojin biyan kuɗaɗe, amma maimakon ya halarta, sai ya aike da tsohon darakta wanda ya zargi kwamitin da neman tozarta hukumar.

Kwamitin ya bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga babban sakataren JAMB da ya bayyana da kansa tare da tawagarsa ranar Talata mai zuwa, don gabatar da dukkan takardun da aka nema, inda aka yi gargadin cewa rashin yin hakan zai sa Majalisar ta yi amfani da ikonta da kundin tsarin mulki ya ba ta a sashe na 88 da 89 na kundin tsarin mulkin 1999.

Wani dan Majalisa, Awaji-Inombek Abiante daga jihar Rivers, ya bayyana cewa ficewar JAMB daga zaman na nuna rashin girmama ikon Majalisar, yayin da Rodney Amboiowei daga jihar Bayelsa ya ce duk wata hukuma mai amfani da kuɗin jama’a dole ne ta bada cikakken bayani ga ’yan ƙasa.

 

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here