Tinubu ya dakatar da shugaban EFCC AbdulRasheed Bawa

Abdulrasheed Bawa
Abdulrasheed Bawa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da yi wa Tattalin Ariƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), AbdulRasheed Bawa.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Tarayya ta ce shugaban ya ɗauki wannan mataki ne domin bayar da damar gudanar da bincike kan wasu manya-manyan zarge-zargen da ke kan Bawa.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin Tarayya, ta ce an bai wa AbdulRasheed Bawa umurnin miƙa aiki ga daraktan gudanarwa na hukumar, wanda zai kula da yadda za a gudanar da binciken.

A shekarar 2021 ne dai tsohon shugaban Najeriya, Muhammdu Buhari ya naɗa Bawa, a matsayin shugaban hukumar ta EFCC.

AbdulRasheed Bawa shi ne jami’i mai girman muƙami da sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar daga aiki bayan kama mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here