Shugaba Buhari ya amince da bai wa gwamna Zulum lambar karramawa ta CON

ZULUM 1
ZULUM 1

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da bai wa gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum lambar girmamawa ta CON, domin karrama shi a matsayinsa mai hidima wa kasa.

Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a wata wasika da ya aikewa gwamnan a birnin Maiduguri.

“Ina da farin cikin sanar da kai cewa Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da a ba ka lambar yabo ta kasa, a matsayin CON ”, Inji Akume.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau ya fitar ta ce ministan, a cikin wasikar mai dauke da kwanan watan Satumba 19, 2022 ta ce za a gudanar da binciken karramawar da safiyar Talata, 11 ga Oktoba, 2022, a dakin taro na kasa da kasa dake Abuja.

Karramawar ita ce mafi girman karramawa da shugabanni na yawancin ƙasashe ke bayarwa ga ƴan ƙasa waɗanda ke ba da gudummawa ta musamman ga ƙasar su.

A ranar Talata 28 ga Agusta 2021, Shugaba Mohammed Bazoum na Jamhuriyar Nijar ya baiwa Gwamna Zulum lambar girmamawa ta kasa wato “de Grand Officer Dans I`Ordre”, wanda yayi daidai da matsayin lambar yabon GCON a Najeriya.

Zulum ayanzu haka yana da lambobin yabo sama da 20 mafi yawansu daga manyan jaridun Najeriya da kuma manyan jami’o’i da cibiyoyin ilimi da suka hada da Jami’ar Ibadan, Kwalejin Kiwon Lafiya ta Kasa ta Kasa, Jami’ar Afe Babalola dake Ado Ekiti da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here