Na damu bisa halin da ƴan Najeriya suka tsinci kai a ciki- Shugaba Buhari

Muhammadu Buhari speaking
Muhammadu Buhari speaking

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa juriya da hakurin da suka nuna babu shakka ba zai tashi a banza ba yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da daukar matakai dan karfafa jami’an tsaro wajen tunkarar kalubalen matsalar tsaron kasar.

Shugaban ya bada wannan tabbacin ne lokacin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya a wani shirin bikin murnar cikar Najeriya shekaru 62 da samun ‘yancin kai daga turawan birtaniya.

“A yayin da muke ci gaba da kokari dan dakile matsalolin tsaro da suka addabe mu a farkon wannan gwamnati, mun fitoda sabbin tsare-tsare, musamman ta fuskar yin garkuwa da mutane, cin zarafi, kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, fashi da makami da sauran su.

“Duk irin wadannan jami’an tsaron mu ne ke magance su.

“Ina mai nuna takaici da dana- sani kan radadi da ‘yan Najeriya ke ciki kuma ina tabbatar muku cewa juriya da hakurinkun da kukayi ba za su kasance a banza ba.”

Ya ce gwamnatin na ci gaba da mayar da hankali da karfafawa jami’an tsaro domin su samu damar tunkarar duk wani kalubalen tsaro.

“A lokacin da aka kafa wannan gwamnati a shekarar 2015, na samar da kudaden ga hukumomin tsaro ke bukata wanda kuma aka inganta a wa’adina na biyu a 2019 domin su samu damar shawo kan matsalolin tsaro.

“Za mu ci gaba a kan wannan tafarki da kokari har sai hakan mu ya cimma ruwa.”

Buhari ya yi bayanin cewa Gwamnatin sa za ta cigaba da kokari domin magance matsalar rashin tsaro tareda aiki tukuru wajen rage tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabas, tsagerun Neja Delta, rikicin kabilanci, addini da sauran matsalolin da ke barazana ga kasar nan.

“Yan uwana ‘yan Najeriya, wannan gwamnatin ta kawar da rashin tabbas na shekaru da dama na masu zuba jari a bangaren mai da iskar gas tare da zartar da dokar masana’antar man fetur, 2021.

“Kun ga an yi hasashen cewa matsalar cutar COVID 19 na tsanantar abubuwa a kasar bai tabbata ba, kasancewar anyi hasashen cewa hakan zai kara sanya wa tattalin arzikinmu tasgaro a kasuwannin duniya ta hanyar hana karuwar hauhawar farashin kayayyaki,” in ji shi.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here