Kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Kano ta kasa NAKSS wadanda ke karatu a jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse a jihar Jigawa, sun bukaci gwamnati jihar Kano da ta duba halin da suke ciki gaza biyan kudinn makarantasu har kawo yanzu sakamakon Karin da aka yi.
Mai Magana da yawun shugaban kungiyar na kasa Ibrahim Yunusa ne ya yi koken inda ya bayyana cewa akwai dalibai da yawa da suka gaza biyan kudin makarantar sakamakon halin da ake ciki.

A cewar Yunusa, a farkon wannan shekara ne hukumar jami’ar ta yi Karin kudin makarantar daga naira dubu 30 ko dubu 40 da ake biya a baya zuwa Naira dubu 100 da doriya.
A dalilin wannan hali da wasu cikin Daliban ke ciki ne ya sanya kungiyar ta NAKSS ta gudanar wata zanga-zangar lumana da nufin janyo hankalin gwamnatin jihar Kano game da halin da wasu cikin daliban ke ciki.

A cewar mai Magana da yawun shugaban kungiyar, duk da yake ita jami’ar FUD ta fitar da tsarin da kowa zai iya biya ta hanyar biyan kaso 60 a zangon farko da kuma biyan kaso 40 a zango na biyu, amma har kawo yanzu akwai wadanda basu biya ba, saboda babu halin hakan.













































