Kungiyoyin NLC da TUC sun jaddada aniyarsu ta tafiya yajin aiki a fadin kasar nan daga ranar Laraba

FGs meeting with NLC ends in Deadlock
FGs meeting with NLC ends in Deadlock

Gamayyar kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun kira taron kwamitin zartarwar kungiyoyin da ba’a saba ganin irin sa ba.

A yayin taron, kungiyoyin kwadagon sun sake tattauna batun yajin aikin da suka shirya biyo bayan dukan shugaban kungiyar NLC na kasa, Joe Ajaero da jami’an tsaro suka yi, inda kuma suka sake nazartar yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar ta rattaba hannu tsakaninsu da gwamnatin tarayya tun a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar 2023, biyo bayan cire tallafin man fetur.

Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta TUC Tommu Etim, ne ya sanar da abubuwan da aka tattauna a yayin taron da kungiyar ta kira ga manema labarai a ranar Talata.

Kungiyar kwadagon dai ta bada wa’adin kwanaki biyar ne cewa za ta shiga yajin aiki a fadin kasar nan, biyo bayan kama Ajaero da jami’an tsaro suka yi a birnin Owerri na jihar Imo.

Kungiyar kwadagon dai ta bukaci da a sauya kwamishinan ‘Yan sandan jihar ta Imo tare kuma da tuhumar mai taimkawa gwamnan jihar bisa zargin su da hannu a kitsa kamu da dukan da aka yiwa Joe Ajaero.

Gamayyar kungiyoyin gwadagon sun kuma jaddada aniyarsu ta tsunduma yajin aiki a fadin kasar nan matukar aka gaza biya musu bukatunsu har zuwa cikar wa’adin kwanaki biyar din suka diba a farko.

An dai kama Ajaero ne tun a ranar Laraba 1 ga watan Nuwambar shekarar da muke ciki ta 2023, yayin da ma’aikata ke tsaka da gudanar da zanga-zanga a fadin jihar Imo, sakamakon kin biyansu albashin su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here