Jami’ar Bayero ta samu karin farfesoshi 34, Nasir Fagge, Abubakar Ahmad, Cikin Wasu da dama

Jami'ar, Bayero
BUK Senate 1

A taron Majalisar gudanarwa karo na 14, Jami’ar Bayero Dake Kano, ta amince da karin girma ga manyan malaman ta 34 zuwa matakin Farfesoshi da mataimakan farfesoshi 56 na shekarar 2020/2021.

Cikin wata sanarwa da mukaddashin darakta gudanarwa ta jami’ar, Binta Yahaya Kofar Na’isa ta fitar ts ta sanyawa hannu, ta ce an amince da daga likafar bayan amincewar zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa wadanda aka daga likafar ta su zuwa mukamin Farfesa sun hada da tsohon shugaban kungiyar malaman jami’o’i, Dakta Nasir Isa Fagge a matsayin Farfesa a fannin kimiyyar nukiliya, Dakta Usman Ibrahim Abubakar Farfesa a fannin yada labarai, da Dokta Salihu Lawal, Shugaban Makarantar Ci-gaba da Ilimi a matsayin Farfesan Nazarin Addinin Musulunci.

Sanarwar ta ce, sauran wadanda aka gabatar a zaman sun hada da Dokta Sani Malami Farfesa a fannin harhada magunguna; Dr Musa Njidda Farfesan Kula da harkokin Wasanni; Dokta Bello Ibrahim Farfesa na Nazarin Laifuka da Tsaro; Dr Kabir Bello Farfesa a fannin ilimin zamantakewa Dr Ya’u Musa Dantata (Farfesa na Ilimin Bukatu na Musamman) da Dr. Aliyu Salisu Barau (Farfesa na Ci gaban Birane da Gudanarwa) da Dr Ibrahim Tajo Siraj (Farfesa na ilimin sinadaran Inorganic Chemistry).

A cewar sanarwar, wadanda aka daga likafar su zuwa matsayin Mataimakin Farfesa sun hada da Dr Bashir Aliyu Umar (Nazarin Musulunci); Dr Hafsat Umar Abdullahi (Ilimi); Nura Ibrahim (Bayanai da Nazarin Sadarwa); Hadiza Jummai Ibrahim (Aikin jarida); Maryam Umar Moukhtar (Aikin Jarida); Bala Boyi Bukata (Bangaren lnjiniyancin jone jonen lantarki); Mohammed Mamodu Maina (Noma da harkokin muhalli) da Abdullahi Yahuza Zainawa (Kimiyyar Siyasa).

Sanarwar ta ce, ”Dukkan nade-naden sun fara aiki daga ranar 1 ga Oktoba, 2021.

Ya ce sauran malaman jami’o’in da suka samu karin girman zuwa matsayin Farfesa, Dokta Suwaiba Sa’id Ahmad, Darakta, Cibiyar Nazarin Jinsi; Dr. Kabir Bello Dungurawa, Shugaban Kano Polytechnic da Dr. Aliyu Dahiru Mohammed Na bangaren tattaki da sauransu.

Cikin waɗannan karawa girma zuwa matsayin Mataimakin Farfesa wanda zai fara aiki daga Oktoba 2020 kuma sune; Dr Ali Abdullahi (Noma); Dr Auwal Sani Salihu (Likitan tabin hankali); Dr Zaharaddeen Garba Habib (Likitan kulada masu tabin hankali) da Dr Musa Usman Umar (Likitan kulada masu tabin hankali.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here