Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2027 a gaban Majalisar Dokokin Jihar a ranar Laraba.
Gwamna Yusuf ya buƙaci mambobin Majalisar Zartarwar Jihar da su yi ƙoƙari wajen nazari da kuma ganin an samu nasarar gabatar da kasafin kuɗin da aka tsara na shekarar 2027, yana mai jaddada muhimmancin haɗin kai wajen ɗaukar nauyi, gaskiya da kuma ingantaccen shugabanci.
Read also: Kanin Sanata Kwankwaso ya rasu
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taro na musamman da Majalisar Zartarwar Jihar ta gudanar a ranar Lahadi.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar.
Gwamnan ya jaddada cewa bai wa mambobin majalisar damar bayyana ra’ayoyinsu cikin ‘yanci tare da yin cikakken nazari kan sassan kasafin kuɗin da aka tsara wa ma’aikatunsu, hukumomi da sauran sassa, zai taimaka wajen samar da ingantaccen kasafin kuɗi wanda ya ƙunshi ra’ayoyin kowa.
Ya umurci Kwamishinan Tsare-tsare da Kasafin Kuɗi da ya jagoranci tattaunawa kan kasafin, yayin da ya buƙaci sauran kwamishinoni da su yi bitar abubuwan da suka shafi ma’aikatunsu domin bayar da gudunmawa mai ma’ana wajen samar da cikakken kasafin kuɗi.
Read also: ‘Ƴan ƙwadago sun kutsa cikin majalisar dokokin Najeriya
A yayin taron, Gwamna Yusuf ya yi maraba da sababbin kwamishinonin da aka rantsar a baya bayan nan zuwa Majalisar Zartarwar Jihar.
Ya tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnatinsa, tare da buƙatar tsofaffin mambobin majalisar da su nuna zumunci ga sababbin kwamishinonin, fahimtar juna da haɗin kai domin ƙarfafa aikin haɗin gwiwa da inganta ayyukan gwamnati a faɗin jihar.
Da yake waiwayar nasarorin da aka samu a ƙarƙashin kasafin kuɗin shekarar 2026, Gwamna Yusuf ya bayyana kyakkyawan fata cewa kasafin kuɗin shekarar 2027 zai samar da sakamako mafi inganci.
Ya bayyana kasafin kuɗin da za a gabatar a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen ƙarfafa nasarorin da aka riga aka samu da kuma hanzarta samun ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.
Haka kuma, ya nuna godiyarsa ga ‘yan jarida bisa ci gaba da ba gwamnatinsa goyon baya, ƙwarewa da haɗin gwiwa.
Read also: DA ƊUMI-ƊUMI: APC ta sanya ranar fara gangamin yaƙin zaɓen shugaban ƙasa
A ƙarshe, Gwamna Yusuf ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa ta hanyar jajirciya, haɗin kai da kuma taimakon Allah, gwamnatinsa za ta ci gaba da cimma manufofinta na ci gaba domin amfanin al’ummar Jihar Kano.













































