Rundunar sojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 2 a Kaduna

rundunar, sojin, Najeriya, kashe, 'yan bindiga, Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani mummunan hari da 'yan bindiga suka yi yunƙurin kaiwa a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar ta hanyar kashe biyu...

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka yi yunƙurin kaiwa a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar ta hanyar kashe biyu daga cikinsu.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Laraba ta ce bayan tattara bayanan sirri, ta yi nasarar yi wa mahara huɗu kwanton ɓauna ɗauke da makamai a yankin Kurmin Aja da ke ƙaramar hukumar Kagarko.

Karin labari: “Batun sakin Nnamdi Kanu baya cikin tattaunawa ta da gwamnonin Kudu maso Gabas” – Obasanjo

“Cikin ƙwarewa dakaru suka yi musu kwanton ɓauna ta hanyar buɗe musu wuta, inda nan take suka kashe biyu daga ciki yayin da sauran suka tsere da raunikan harbin bindiga,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa bayan fafatawar ne kuma aka gano bindigogi ƙirar AK-47 biyu, da ƙunshin harsasai 30, da babur biyu na ‘yan bindigar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here